8 Nuwamba 2020 - 12:08
Iran Ba Za Ta Taba Yarda Da ‘Yan Leken Asirin Isra’ila Da Kuma Masu Kafirta Mutane A Kan Iyakanta ba

Kakakin rundunar sojin kasar Iran Birgediya Janar Abolfazl Shekarchi ya ja kunnen kasashen Armeniya da Azarbaijan da suke yaki da juna cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba amincewa da kafa sansanin leken asirin Isra’ila da na ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi a kan iyakokin arewa maso yammacin kasarta ba.

ABNA24 : Janar Shakarci ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da kafar watsa labaran Mizan ta kasar Iran inda ya ce: Tuni mun bukaci bangarorin da suke yaki a yankin Nagorno-Karabakh da kada su bari ‘yan takfiriyya su shigo yankin. Don kuwa Iran ba za ta taba amincewa da kasantuwar ‘yan Takfiriyya a kusa da ita ba.

Har ila yau kuma kakakin sojin ya ja kunnen kasashen biyu dangane da batun sansanonin leken asirin Isra’ila a wajen, inda ya ce Iran ba za ta taba amincewa da kafa sansanonin leken asirin Isra’ila a kusa da kan iyakokinta ba. Inda ya ce duk wata kasar da ta bari wadannan abubuwa biyu suka faru a cikin kasarta, to kuwa ita ce za ta dau alhakin dukkanin abin da zai biyo baya.

A karshe karshen watan Satumban wannan shekarar ne dai wani sabon yaki ya barke tsakanin kasashen Armeniya da Azarbaijan kan yankin nan na Nagorno-Karabakh bayan da ‘yan aware na yankin suka so balle shi daga kasar Azarbaijan, inda ya wuce yanzu daruruwan mutane da suka hada da sojoji da fararen hula suka rasa rayukansu sakamakon rikicin.

Wasu rahotanni suna nuni da cewa kasar Turkiyya wacce take goyon bayan kasar Azarbaijan ta dauko wasu sojojin sa kai ‘yan takfriyya da take da su a kasar Siriya ta dawo da su kasar Azarbaijan don taya gwamnatin yaki, kamar yadda kuma wasu rahotanni suke nuni da kokarin Isra’ila ta tabbatar da ‘yan leken asirinta a yankin da ke makwabtaka da Iran.

342/